12 Yuli 2021 - 12:21
​ Siriya Ta Yaba Da Kudirin MDD, Kan Fadada Ayyukan Agaji

Kasar Siriya ta yaba da kudurin Majalisar Dinkin Duniya na baya bayan nan kan fadada ayyukan ba da agaji a iyakokin kasar.

ABNA24 : Da yaka bayyana hakan ministan harkokin wajen Syria ya yaba da matakin wanda ya danganta da nasara.

Hakan a cewar Faisal al-Mekdad, zai tilastawa kasashen yamma su mutunta 'yancin yankunan Siriyar.

A ranar Asabar ne Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya zartar da kuduri mai lamba 2585 na tsawaita izinin aikin ba da agaji ga 'yan Syria har na tsawon watanni 12.

Kudurin, wanda ya sami goyon baya daga mambobin majalisar 15, zai ba da damar ba da taimako ta kan iyakokin zuwa Syria daga kan iyakar Bab al-Hawa na kasar da Turkiyya har zuwa ranar 10 ga Janairun 2022, sannan kuma a kara shi, sannan kuma a kara shi zuwa wasu watanni shida har zuwa 10 ga Yuli, 2022.

Za a bukaci sakatare janar na MDD, ya yiwa kwamitin tsaro bayani kowane wata tare da gabatar da rahoto kan aiwatar da kudurin.

Rahoton zai kuma bayar da cikakkun bayanai kan ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya da ke kan iyakoki, da suka hada da na rarraba kayan, da yawan wadanda suka amfana, da abokan aiki, da wuraren da ake isar da kayan agaji a matakin gundumomi, da kuma yawan abubuwan da aka gabatar.

342/